Kotun Masar ta dage yanke hukunci

Kotun tsarin mulki ta Masar
Image caption Kotun tsarin mulki ta Masar

Babbar kotun tsarin mulki a kasar Masar ta dage wasu muhimman hukunce-hukunce biyu wadanda aka shirye za ta yanke a yau Talata.

An sa ran kotun za ta yanke hukunci kan ko za a rusa majalisar dattawan da masu kishin Islama suka mamaye, bayan zargin da aka yi na saba ka'idojin zabensu.

Sai dai a maimakon haka, kotun ta mika batun ga wani kwamitin da ke ba ta shawara.

An kuma yi tsammanin za ta yanke hukunci kan halarcin kwamitin da ya tsara sabon kundin tsarin mulkin kasar - wanda shi ma masu goyon addinin Islama suka fi rinjaye.

A yanzu za a duba batutuwan ne a wani zama da kotun za ta yi a watan gobe.

Karin bayani