Mutane 19 sun mutu a hatsarin jirgin kasa a Masar

Image caption Jirgin kasan da ya yi hatsari a Masar

Wani jirgin kasa da ya yi hatsari a Masar ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla goma sha tara tare da jikkata wasu da dama.

Jirgin dai ya kwaso jami'an sojoji sababbin dauka ne wadanda za su je kudu maso yammacin birnin Alkahira.

Wannan dai shi ne na baya-bayan nan daga jerin haduran jiragen kasa da ke faruwa a kasar ta Masar.

A watan Nuwamba kusan yara hamsin ne 'yan makaranta suka rasa rayukansu a lokacin da wani jirgin kasa ya yi karo da motar da take dauke da su.

Karin bayani