Najeriya za ta tura sojoji 900 zuwa Mali

Dakarun Sojin Najeriya
Image caption Tuni dakarun Faransa suka fara kai hare-hare kan 'yan tawayen

Gwamnatin Najeriya ta ce ta kammala shirin tura rundunar sojojinta zuwa kasar Mali, a ranar Alhamis don tallafa wa Sojojin kasar wajen kwato yankin arewaci da 'yan tawaye su ka mamaye.

Rundunar za ta kunshi kusan sojoji dari tara da kayan yaki ciki har da jiragen sama.

Mai magana da yawun hedikwatar tsaron Najeriya, Kanar Mohammaed Yarima ya shaidawa BBC cewa shugaban Najeriya ne ya bada umarnin aikewa da balatiyar soji daya da karin wasu 'yan kadan, kuma gabakidaya sojoji kusan dari tara ne zasu je Kasar Malin .

Amma yace yanzu bataliyar soji guda za a soma aikewa wacce zata kunshi sojoji kusan dari biyu.

Ya kara da cewa sun kammala dukkanin shirye shiryen da ya kamata domin samun nasarar wannan aiki.

Karin bayani