Zanga-zangar nuna kyamar cin hanci a Pakistan

Image caption Tahir-ul Qadri

Jami'an tsaro a Pakistan sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kulake wajen tarwatsa dubban masu zanga-zangar kyamar cin hanci da rashawa a kasar.

Masu zanga-zangar sun yi kokarin shiga ginin majalisar dokokin kasar da ke birnin Islamabad.

Wani shahararren malamin Sufi na kasar, Tahir-ul Qadri, wanda ya jagoranci zanga-zangar ya ce shi da magoya bayansa za su ci gaba da kasancewa a birnin sai sun cimma burinsu.

Yana so ne a rusa gwamnati sannan a dage zaben da ake shirin gudanarwa har sai an magance rashawa da cin hancin da ya ce sun yi wa kasar katutu.

Masu sukar malamin sun ce sojojin kasar ne ke mara masa baya sai dai ya musanta zargin.

An baza dubban 'yan sanda a kan titunan birnin Islamabad don sanya idanu a kan abubuwan da ke faruwa.

Karin bayani