Wasu kamfanonin jiragen sama sun dakatar da jigila a Japan

Image caption Jirgi samfurin Boeing 787

Kamfanonin jiragen sama biyu da suka fi girma a Japan sun dakatar da tashin dukkanin sababbin jiragen su samfurin Boeing 787 da ake kira dreamliner, bayan wani jirgi ya yi saukar gaggawa lokacin da aka ga hayaki na fita daga cikinsa.

A makon da ya gabata ne hukumomin kula da harkokin jiragen sama na Amurka suka bayar da umarnin a sake duba tsarin jirgin, bayan ya fuskanci matsalolin da suka hada da zubar mai, da fashewar gilashin tagar sa, da matsalar birki da kuma tashin wuta.

Kamfanin kera jirgin sama na Boeing ya dora burinsa sosai a samfurin jirgin na 787, wanda yake tattare da nau'in fasahohi daban-daban da kuma kayan kira na zamani.

Karin bayani