Majalisar Jumhuriyar Nijar ta amince da tura sojoji Mali

Shugaba Mahamadou Issoufou
Image caption Nijar tana kan gaba gaba wajen ganin an dauki matakin soja a Mali

Majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar ta kaɗa ƙuriar amincewa da kudurin gwamnatin ƙasar na tura sojoji 500 zuwa Mali domin yaƙar 'yan tawaye.

Tuni dai ƙasashen yammacin Afrika da dama ciki harda Najeriya suka amince su tura sojoji Mali a wani bangare na rundunar ƙungiyar raya tattalin arzikin yankin ta Ecowas ko Cedeao.

Majalisar ta Nijar ta amince da kudurin ne da gagarumin rinjaye, sai dai duk da haka, wasu 'yan majalisar su hudu sun nuna adawa da shirin.

Sojojin Faransa sun shafe kwanaki shida suna lugudan wuta kan 'yan tawaye masu kishin Islama da suka ƙwace iko da arewacin Mali tun farkon shekarar da ta gabata.

Kungiyar 'yan tawayen ta Ansaruddin ta kafa tsarin shari'ar Musulunci a yankin.

Sai dai kasashen duniya sun zarge su da take hakkin bil'adama da kuma rusa hubbaren malaman Sufanci a garin Tumbuktu da kuma sauran sassan ƙasar.

Karin bayani