Obama ya nemi goyon bayan majalisar dokoki kan batun haramta mallakar bindigogi

Obama da mataimakinsa Biden
Image caption Mr Obama ya ce shirin zai yi aiki ne idan Amurkawa sun goyi bayan sa

Shugaban Amurka Barack Obama, ya yi kira ga majalisar dokokin ƙasar da ta dawo da dokar da ta haramta mallakar manyan bindigogi a ƙasar.

Shirin shugaban ya hada da hana amfani da bindigogin da ke daukar harsasai fiye da goma da kuma gudanar da bincike kan mutanen da ke son sayen bindiga.

Sai dai shugaban ya ce wannan ba zai faru ba sai Amurkawa sun goyi bayan shirin.

Mr Obama ya ce yana goyon bayan damar mallakar makamai da tsarin mulki ya bayar, amma ya ce harbe-harben da ake yi yana take hakkin mutane na rayuwa da kuma 'yanci.

Karin bayani