'An kammala aikin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a Algeria'

Image caption Matatar hakar iskar gas a Algeria

Rahotanni daga Algeria sun ce sojojin kasar sun kammala farmakin da suke kaiwa a yunkurin ceto 'yan kasashen wajen da masu kishin Islama suka yi garkuwa da su a wata matatar iskar gas da ke gabashin kasar.

Sai dai gidan rediyon gwamnatin kasar ya ambato wadansu jami'ai na cewa dakarun soji na musamma na ci gaba da yi wa matatar kawanya, inda masu tayar da kayar-bayan ke ci gaba da yin garkuwa da mutanen da suka kama.

Hukumomin kasar sun ba da rahoton kisan mutane daga bangarorin biyu.

Masu fafutikar sun ce an kashe wadanda ake garkuwar da su guda 35 da kuma masu garkuwar guda 15 a hare-haren da soji suka kai ta sama, sai dai hukumomin ba su tabbatar da hakan ba.

A lokacin da take hira da manema labarai a Washington Sakatariyar Wajen Amurka, Hillary Clinton, ta ce kasarta ta sha alwashin murkushe kungiyoyin masu yin garkuwa da mutane.

A ranar Laraba ne dai masu kaifin kishin Islama da ake alaƙantawa da ƙungiyar al- Qaeda suka kai hari a kan matatar iskar gas ɗin tare da mamaye ta.

Karin bayani