Sojojin Algeria sun yi wa masu garkuwa da mutane kawanya

Image caption Cibiyar hakar gas a Algeria

Sojojin Algeria sun yi wa wata cibiyar hakar gas a gabashin kasar kawanya bayan 'yan bindigar da ake alakantawa da masu kishin Islama sun kai hari sannan suka yi garkuwa da 'yan kasashen waje da dama.

Wadansu rahotanni sun ce dakarun kasar sun fafata da masu tayar da kayar-bayan a daren ranar Laraba.

Masu kishin Islaman dai sun ce suna rike da fiye da mutane arba'in koda yake ma'aikatar harkokin wajen kasar ta ce mutanen ba su kai haka ba.

Wadansu rahotanni na cewa sun kashe biyu daga cikin mutanen da suka kama, ciki har da dan Burtaniya.

Algeria ba za ta ba da kai bori ya hau ba

Rahotanni daga kafafen watsa labaran Faransa sun ce masu garkuwa da mutanen na so ne a saki masu kaifin kishin Islama guda dari da ake tsare da su a gidajen yarin Algeria.

Ministan ma'aikatar, Dahou Ould Kablia, ya ce gwamnatin kasar ba za ta bayar-da-kai-bori-ya-hau-ba.

Kasashen da aka yi garkuwa da 'ya'yansu sun yi Alla-wadai da matakin.

Karin bayani