"An kashe 'yan kasashen waje a Algeria"

Masana'antar haƙar iskar gas a Algeria
Image caption Algeria na haƙo iskar gas ne tare da wasu ƙasashen waje

Rahotanni daga Algeria sun ce an kashe akalla mutane 34 da aka yi garkuwa da su da kuma 14 daga cikin wadanda suka yi garkuwar da su, sai dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da hakan.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an samu hasarar rayuka da dama a yankin - inda wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da ma'aikatan mai yawancinsu 'yan kasashen waje.

Tunda farko kafofin waatsa labaran Aljeriya sun ce 'yan kasashen waje goma sha biyar da 'yan kasa talatin, sun sami tserewa daga ma'aikatar iskar gas din.

Rahotannin farko sun ce sojin Aljeriya da suka yi wa wurin kawanya sun yi musayar wuta da manyan bindigogi da masu garkuwar.

'Yan kasashen wajen da ake garkuwa da su sun fito ne daga Burtaniya, da Faransa, da Amurka, da Norway, da kuma Japan.

Muna dauke da karin bayani.

Karin bayani