Algeria ta ce an 'kammala' aikin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su

Matatar iskar gas a Algeria
Image caption Ranar Laraba ne aka kai hari a kan matatar iskar gas ɗin tare da mamaye ta

Kamfanin dillancin labaran Algeria, mallakin gwamnati, ya ce an 'kammala' aikin ceto mutanen da aka yi a garkuwa da su a wata matatar iskar gas dake gabashin ƙasar.

An bada rahoton ceto 'yan ƙasashen waje hudu , amma an kashe 34 daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su da kuma 14 daga cikin masu kaifin kishin Islama da suka kama 'yan ƙasashen wajen da kuma 'yan Algeria dake aiki a wurin.

Gwamnatin Birtaniya ta ce an fada ma ta cewa har yanzu ana cigaba da bincika matatar iskar gas ɗin, kuma baa tabbatar da yawan wadanda suka rasa rayikansu ba.

Wakilin BBC ya ce har yanzu gwamnatin Birtaniyar na dakon samun bayanai daga gwamnatin Algeria a game da yawan 'yan Birtaniyar da aka kashe da wadanda suka samu raunika da kuma wadanda suka ɓata.

A ranar Laraba ne dai masu kaifin kishin Islama da ake alaƙantawa da ƙungiyar al- Qaeda suka kai hari a kan matatar iskar gas ɗin tare da mamaye ta.

Karin bayani