Dakarun Algeria na kaddamar da hari kan masu kishin Islama

Algeria
Image caption Ana kai hari kan matatar gas inda akai garkuwa da mutane

Dakarun Algeria na kaddamar da farmaki akan mayaka masu kaifin Kishin Islama wadanda sukai garkuwa da 'yan kasashen waje da 'yan kasar Algerian a wata matatar gas

An bada rahotan cewa an samu jikkata a cikin wadanda aka sacen da kuma 'yan bindigar

Wani kamfanin dillacin labaru na Mauritania ya ambato Majiyoyin soji na cewa an kashe wadanda aka sace su talatin da biyar da kuma masu sace mutanen su goma sha biyar a hare haren da jiragen helikoptar soji su ka kaddamar ta sama

Sai dai ba a tabbatar da rahotannin ba kawo i yanzu

Kamfanin dillacin labaru na Algeria yace sojoji sun yi harbi akan wasu motoci biyu dake dauke da 'yan bindigar lokacin da suke kokarin tserewa

Kafar yada labaran tace an saki baki 'yan kasashen waje akalla guda hudu da aka sace

Karin bayani