Faransa ta kara yawan dakarun ta dake Mali

Dakarun Faransa a Mali
Image caption Sojin Faransa dubu daya da dari hudu su na Malli

Faransa tace yawan dakarun da ta tura zuwa Mali ya karu zuwa dubu daya da dari hudu.

Faransa dai tana cigaba da kara yawan dakarunta, tun daga lokacin da sojanta suka soma isa Mali kasa da wata guda da ya gabata.

Shirin Faransa dai shi ne ta aika dakarunta dubu biyu da dari biyar zuwa Mali, wacce tayi wa mulkin mallaka, domin tallafa musu wajen kwato yankunan arewacin Mali daga masu kaifin kishin Islama.

Karin bayani