Shugabannin ECOWAS na yin taro a kan Mali

Image caption 'Yan tawayen Mali

A ranar Juma'a ne shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS za su gudanar da taro a kasar Ivory Coast inda ake sa ran za su cimma matsaya game da batun gaggauta tura dakarun sojoji kimanin dubu uku zuwa kasar Mali.

Kazalika shugabannin za su tattauna kan yanayin da ake ciki a kasar Guinea-Bissau tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Aprilun shekarar 2012.

Shugabannin dai sun yi kokarin ganin an warware matsalar cikin ruwan sanyi amma lamarin ya gagara.

Daga bisani ne kungiyar ta nemi tallafin kungiyar tsaro ta NATO don kawar da masu tayar da kayar baya a kasar ta Mali.

A ranar Alhamis ne daukacin mambobin Majalisar Dokokin Najeriya suka amince da bukatar da shugaban kasar ya gabatar musu ta neman aikewa da sojoji 1,200 fiye da adadin da kasar ta ce za ta aike da su kasar Mali tun da farko.

Kazamin fada a Mali

Ana can ana ci gaba da gwabza kazamin fada a Mali inda dakarun Faransa da takwarorinsu na Mali ke kokarin dakile fadada ikon masu kaifin kishin Islama a arewacin kasar.

Da dama daga cikin dakarun Faransa suna garin Segou da ke arewa maso gabashin babban birnin Mali, Bamako, inda suke lura da wata gada da ta ratsa Kogin Kwara, wacce dole ne sai 'yan tawayen sun tsallaka ta kafin su iya cimma garin.

Karin bayani