Sojojin Najeriya sun tashi zuwa Mali

Dakarun Najeriya
Image caption Dakarun Najeriya kafin su shiga jirgi zuwa Mali

Kashi na farko na sojojin Najeriya su kusan dari da casa'in sun tashi zuwa Mali, inda za su bi sahun takwarorinsu na Faransa wadanda ke fafatawa da 'yan tawaye masu tsattsauran ra'ayin addinin Musulunci.

Fiye da dakaru dubu uku ne daga kasashen Yammacin Afirka ake sa ran za su taka rawa a yunkurin kwato arewacin Mali daga hannun 'yan tawayen.

Najeriya dai ta yi alkawarin bayar da dakaru dari tara da wasu jiragen saman yaki.

Nan ba da jimawa ba ne dai kashi na farko na sojojin Najeriyar za su fara tashi zuwa kasar ta Mali daga Kaduna, inda ake gudanar da wani biki na bankawana da su.

Karin bayani