Sabuwar taƙaddama a matatar man fetur ta Nijar

Matatar man SORAZ
Bayanan hoto,

Nijar ta fara taace man fetur ne a shekara ta 2011

A jamhuriyar Nijar, wata taƙaddama ce ta kunno kai tsakanin ma'aikatan kamfanin taace man fetur na ƙasar, SORAZ da shugabannin kamfanin, a kan batun gina wa ma'aikatan wani rukunin gidaje guda dari da goma a birnin Damagaram.

Ma'aikatan dai sun yi zargin cewa ba a saka su ba a cikin kwamitin dake kula da batun gina gidajen, saboda haka sun nemi da a rushe shi.

Haka kuma sun koka cewa ministan mai na ƙasar, Mallam Foumakoye Gado ya ƙi ya gaana da su domin gabatar masa da buƙatunsu, bayan da ya ƙaddamar da aikin aza tubalin farko na gina gidajen.

Sai dai shugabannin kamfanin na SORAZ sun ce ma'aikatan ba su bi ƙa'ida ba wajen ganin ministan, kuma za a duba korafin da suka yi na cewa ba sa cikin kwamitin dake sa ido a kan gina gidajensu.