SSS ta yi gargadi kan aikata laifufuka da sunan Boko Haram

Sojoji na binciken wasu da suke zargi
Image caption Matsalar tsaro ta fi ne ƙamari a Arewacin Najeriya

Hukumar jami'an tsaro masu farin kaya a Najeriya, SSS, ta ce ta gano wasu gungun ɓata gari dake amfani da sunan ƙungiyar Jama'atu Ahlilsunna Lilda'awati wal Jihad da wasu ke kira Boko Haram, wajen damfarar al'umma.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta aika wa manema labarai inda ta ce ta kama mutane biyu da take zargi da irin wannan laifi, kuma nan da ba da jimawa ba za ta gurfanar da su a gaban kotu.

Haka kuma Hukumar ta SSS, ta bai wa Jama'atu Ahlilsunna Lilda'awati wal Jihad shawara da su yi wa Allah su yi wa Annabi su ajiye makamai su rungumi tayin hawa teburin sulhu da Gwamnatin Tarayya.

Har ya zuwa yanzu dai ƙungiyar ta Jama'atu ahlulsunna lilda'awati wal Jihad ta ƙi ta zauna a teburin shawarwari da gwamnati saboda a cewar ƙungiyar, gwammatin ta yaudare ta a baya.

Karin bayani