'Har yanzu ana tsare da mutane a Algeria'

Matatar Gas
Image caption Matatar gas din tana kudancin kasar ta Algeria

Kafafen yada labarai a Algeria sun ce kimanin mutane 650 aka kubutar daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su a Algeria, amma har yanzu ba a san inda 'yan kasashen waje 60 suka shiga ba.

Kamfanin dillancin labarai na kasar APS, ya ce wadanda aka kubutar a matatar iskar gas din ta Amenas sun hada da 'yan kasar ta Algeria 573 da kuma fiye da rabin 132 'yan kasashen waje.

Har yanzu 'yan bindigar na yankin, a cewar APS. "Wani abu da ke jan hankali" shi ne akwai 'yan Burtaniya kasa da 30 da ake kyautata zaton ana tsare da su.

Akalla ma'aikata 'yan kasashen waje hudu ne suka mutu lokacin da dakarun Algeria suka kai hari matatar ranar Alhamis.

'Ba su da wata hujja'

Kawo yanzu babu "cikakken adadin wadanda ake tsare da su sannan rahotanni sun ce wasunsu sun nemi mafaka a wasu sassan matatar.

Fira Ministan Burtaniya David Cameron ya ce ya yi wa Algeria tayin gudummawar kayan aiki domin su fuskanci matsalar, sannan ya tuntubi shugabannin kasashen da abin ya shafi mutanensu.

Ya shaida wa majalisar dokokin kasar cewa yawan 'yan Burtaniya da ke cikin hadari ya ragu daga 30 kamar yadda aka ce tun da fari.

"Muna bukatar musan alhakin wanna abun a wuyan wa ya rataya, 'yan ta'adda su ke da alhakin wannan hari da salwantar rayuka. Ba su da wata hujja ta sace mutanen", a cewar Mr Cameron.

A yanzu dai ba a gudanar da aikin hakar gas din a matatar domin kaucewa hadarin fashewar gas.

Karin bayani