Yadda hare-haren Boko Haram suka sauya Kano

Hare-hare a Kano
Image caption Hotuna irin wadannan sun zama ruwan dare a birnin na Kano

Ranar 20 ga watan Janairu dai rana ce da mazauna birnin na Kano ba za su manta da ita ba, domin kuwa a yammacin ranar ne kungiyar Jama'atu Ahlisuunah Lidda'awati Wal Jihad (Boko Haram) ta kaddamar da hare-hare mafi girma da muni a kasar.

Lamarin dai ya tayar da hankulan mazauna birnin Kano da ba su taba gamuwa da irin sa ba, abinda kuma cikin dan kankanin lokaci ya tsaida al'amura cik a birnin da yafi kowanne hada-hada a arewacin Najeriya, sannan ya bude kofar wasu hare-haren.

Hare-haren da aka kai kimanin ofisoshin jami'an tsaro da dama ciki har da ofishin shiyya ta daya na rundunar 'yan sandan Najeriya sun janyo mutuwar kimanin mutane 200 a cewar alkaluman hukumomi, sai da mazauna birnin na ganin adadin ya fi haka matuka.

Hare-haren da matakan hukumomi da kuma zaman dar-dar da jama'a ke yi sun durkusar da al'amura a jihar musamman ma na kasuwanci.

Kasuwanci ya takaita

An dai dauki sa'o'i da dama ana jefa abubuwan fashewa a wuraren da aka kai hare-haren, gami da musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da kuma maharan a wasu daga cikin wuraren da lamarin ya shafa.

"Kara da karfin fashewar abubuwa sun sa gidajenmu sun girgiza, yayin da karar bindigogi suka tilasta wa mutan gida na kwanciya a kasa dan tsira da ransu," a cewar Nasuru Sa'idu Adhama makoci ga Hedkwatar 'yan sandan Kano daya daga wuraren da lamarin ya fi kamari.

Hare-haren sun sa gwamnati sanya dokar takaita zirga-zirga, sannan jami'an tsaro suka fara kafa wuraren binciken abubuwan hawa, wanda jama'ar birnin basu saba da su ba.

Image caption Hare-haren dai sun hada da na kunar bakin wake da akan kai da motoci

'Yan kasuwa da dama da ke zuwa jihar daga wasu jihohin da ma wasu kasashen domin sayayya sun dakatar da zuwa, sabo da fargaba da kuma zargin cin zarafi daga jami'an tsaro.r

Bude kofar hare-hare

"Bakin da ke zuwa wajena domin sayayyar kaya sun yi matukar raguwa saboda abin da ke ya faru a Kano", a cewar Nura Ahmad wani dan kasuwa.

Daya daga cikin shugabannin 'yan kasuwar Kantin Kwari ya ce kafin hare-haren na Janairun 2012, a kullum ana cinikin kimanin naira biliyan hudu a kasuwar, amma a 'yan watannin da suka biyo bayan harin ba a wuce cinikin naira miliyan 300.

Harin na ranar 20 ga Janairu ya bude kofar hare-hare kala da daban-daban a birnin na Kano da kewaye, abinda ya kara lalata al'amura.

Na baya-bayan nan shi ne wanda 'yan bindiga suka kai kan ayarin motocin Sarkin Kanon Alhaji Ado Bayero, inda suka kashe direbansa da dogaransa biyu, sai dai Sarkin ya tsira da ransa.

Turin babur....

Baya ga bangaren kasuwanci, lamarin hare-haren ya kuma shafi makarantun da ake karatuttuka bayan sallar Magriba.

Daruruwan Masallatai sun dakatar da karatu ala tilas saboda dokar hana fita.

Lamarin rashin tsaron ya kuma shafi harkokin zamantakewa ta fuskoki da dama, domin kuwa hatta bukukwa sun samu sauyin lokaci da takaitar su sabanin yadda yake a al'adance.

Masu babura kuma a birnin na Kano sun gamu da wani sabon salo inda dole ne idan suka doshi wajen da jami'an tsaro ke binciken abubuwan hawa su sauka su tura, sai sun wuce sannan su hau.

Sai dai kawo yanzu shekara guda bayan fara hare-haren, al'amuran kasuwanci sun fara farfado wa, inda baki ke zuwa, sai dai har yanzu 'yan kasuwa na korafi.

Kuma fargabar da jama'a ke da ita ta ragu kasancewar lamarin tsaro na kara inganta, kuma batun ya fara zamewa jama'a jiki.

Haka kuma ana samun raguwar zargin da ake wa jami'an tsaro na muzgunawa jama'a, ko da dai har yanzu wasu jama'ar na ci gaba da korafin ci musu zarafi da jami'an tsaron ke yi.

Babu shakka mazauna birnin na Kano na fatan ganin karshen wannan bala'in da ya dabaibaye jihar da ma sauran sassan Najeriya, sai dai fata ne kawai, domin babu tabbas kan ranar da birnin zai koma kamar yadda yake kafin 20 ga watan Janairun 2012.

Idan kana zaune a Kano, gaya mana yadda wadannan hare-hare suka sauya rayukarka. Shin sun taba ritsa wa da kai?

Karin bayani