Mali: 'Yan tawaye sun fice daga garin Diabaly

Image caption Mayaƙa masu kaifin kishin Islama a Mali

Hukumomi a tsakiyar Mali sun ce masu kaifin kishin islama sun bar garin Diabaly wata guda bayan sun kwace iko da garin. Tun da fari dakarun sojin faransa sun yi wa garin liguden wuta.

'Yan tawayen sun bar garin Diabaly sa'o'i kaɗan bayan da sojojin Mali suka sake karɓe iko da garin Konna.

A ɓangare daya kuma hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar ɗinkin duniya ta ce ta samu rahotannin da ke cewa 'yan tawaye na cin zarafin al'umma a arewacin Mali.

Mai magana da yawun hukumar bada agaji ta majalisar ɗinkin duniya Melissa Fleming ta ce hukumar na shirin aikewa da mutane domin su taimaka.