Pakistan: an tsinci gawar mai bincike

Image caption Ana kokarin dauke gawar Kamran Faisal

Hukumomi a Pakistan sun ce, a birnin Islaamabad an tsinci gawar jami'in da ke binciken zargin aikata almundahana da ake yiwa Prime Ministan kasar Raja Pervez Ashraf.

An tsinci gawar Kamran Faisal a ɗakinsa da ke masauƙin gwamnati inda yake zama.

Babban jami'in 'yan sanda na Islamabad, Bani Amin ya ce abin ya yi kama da ya kashe kansa ne, amma an cigaba da bincike.

Sai dai 'yan uwan Mr Faisal sun ce ba za ta taɓa yiwuwa ya kashe kansa ba, a dan haka kashe shi aka yi.