Algeria: An kashe mutane 12

Image caption Inda akayi garkuwa da mutane a Algeria

Kamfanin dillancin labaran Algeria ya ce a yanzu an tantance mutane a kalla sha-biyu 'yan kasar waje da 'yan Algeria wadanda aka yi garkuwa da su aka kashe tun lokacin da mayakan 'yan kishin Islama suka fara kai samame na kame mutanen da suke garkuwar da su a kamfanin sarrafa iskar gas.

Faransa da Amurka kowacce ta tabbatar da cewa akwai 'yan kasashen su dai-dai dake cikin mutanen da aka kashe.

Rahoton na Algeria ya ce koda yake an saki 'yan kasar wajen kimanin dari daya da aka yi garkuwar da su, akwai mutane talatin da har yanzu ba aji duriyar su.

Wani dan kasar Algeria da aka yi garkuwa da shi, ya samu damar tserewa ya ce, sojojin suna kai hari a kan 'yan ta'addan.

Karin bayani