Ana zaman zulumi a wani bangaren Kasar Burma

Kachin, Burma
Image caption Zaman zulumi a Burma

An bada rahotan zaman dar dar a wani bangare na Kasar Burma, bayan wani farmaki da soji suka kai akan 'yan tawaye na wasu 'yan tsirarun kabilu , sa'oi bayan da gwamnatin Burman ta ayyana tsagaita wuta

Wani wakilin BBC wanda yake a inda 'yan tawayen suke da karfi na yankin Kachin dake Laiza, dake kusa da kan iyakar Kasar china, yace an samu lafawar jin karar harbe harben bindigogi a can, amma mayakan 'yan tawayen na cike da tsoro

Wannan rikici da aka jima ana yi ya sake kunno kai ne a shekarar 2011

Karin bayani