An kai hari kan ayarin motocin sarkin Kano

Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero
Image caption Mutane da dama sun samu raunuka a harin

Wasu 'yan bindiga a Najeriya sun kai hari kan ayarin motocin Sarkin Kano Dr Ado Bayero, inda suka kashe mutane biyar tare da raunata wasu da dama.

Sarkin dai ya tsira da ransa, amma an kashe direbansa da kuma dogaransa guda biyu. Sannan wasu da dama suka samu raunuka ciki har da 'ya'yan Sarkin guda biyu.

Birnin Kano ya sha fuskantar hare-haren 'yan bindiga wadanda a wasu lokutan kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram ke daukar nauyi, sai dai kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin harin na baya-bayan nan.

Dr Ado Bayero na daya daga cikin sarakunan gargajiyar da ke da karfin fada aji da kuma farin jini a arewacin Najeriya, kuma wannan harin ya firgita jama'a sosai arewacin kasar.

'cikin koshin lafiya'

Wasu mutane ne akan babura da kuma mota suka bude wuta kan tawagar Sarkin lokacin da yake dawowa daga masallacin Murtala inda ya halarci saukar karatun Alkur'ani a unguwar Hausawa.

"Mummunan abu ya faru lokacin da wasu 'yan bindiga suka budewa tawagar Sarkin Kano wuta lokacin da yake dawowa daga bikin karatun Alkur'ani", kamar yadda gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso ya shaida wakilin BBC Yusuf Ibrahim Yakasai.

"An kashe mutane uku a tawagarsa, amma shi babu abinda ya same shi, tuni ma naje na gaida Sarkin, wanda yake cikin koshin lafiya," a cewar gwamnan.

Sarkin mai shekaru 80 da wani abu a duniya, ya shafe kusan shekaru 50 yana kan karagar mulki, kuma masana na cewa "ba kasafai yake tsoma baki a al'amuran siyasa ba".

Shekara guda kenan bayan harin farko da aka kai a jihar ta Kano wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 200.