Ana gudanar da taro kan rikicin Mali a Abidjan

Wata tattaunawa akan Mali
Image caption Ana tattaunawa akan rikicin Mali a Abidjan

Shugabannin kasashen Yammacin Afrika sun soma ganawa a Abidjan, babban birnin kasuwancin kasar Kot Divuwa, don tattauna tashin hankalin da ake fama da shi a Mali.

Shugabannin kasashen su goma sha wani abu ne tare da ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius, halartar taron.

Ana yi taron ne game da tura sojojin kasashen yankin zuwa Mali don shawo kan tawayen da ake yi a can.

Karin bayani