ECOWAS ta nemi goyan bayan Kasashe kan rikicin Mali

Taron ECOWAS
Image caption An yi taro kan rikicin Mali

Shugabannin kasashen Yammacin Afrika da ke taro a Kot Divuwa sun yi kiran samun karin goyon baya a abin da suka bayyana da yaki da ta'addanci.

Shugaban Kot Divuwa, Alassane Ouattara, wanda ke jagoran kungiyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS, ya ce ya kamata manyan kasashe su nuna goyon bayansu ga Faransa a yakin da take yi da masu kishin Islama.

Shugaban ya ce, "An gaggauta yadda ake tunkarar matsalar kasar Mali ne ba zato ba tsammani, abin da ke bukatar tilas mu sake hanyar da muke da ita ta kawar da ta'addanci a yankin Sahel.

Tilas mu sa hannu domin babu batun farfadowar tattalin arziki, babu kuma wata nahiya ta duniya da za ta zauna lafiya idan yankin na Sahel ya fada hannun da bai dace ba," a cewarsa.

Karin bayani