Laifukan rikicin Syria ka iya shiga kotun Duniya

Image caption Zubar da jinin da ake yi a Syria

Babbar Jami'ar hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya Navi Pillay ta sake yin kira ga kwamitin sulhu na Majalisar ya gabatar da rikicin da ake yi a Syria gaban Kotun hukunta miyagun laifuka ta duniya.

Da take magana lokacin da aka samu shaidar da ta nuna an yi wa wasu mutane kisan kiyashi a arewacin birnin Homs, Mrs Pillay ta sake jaddada cewar an kashe a kalla mutane dubu sittin a yakin da ake yi a Syria.

Kasashe hamsin da takwas da suka hada da kasashe biyu masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun na Majalisar Dinkin Duniya watau Brittaniya da Faransa sun goyi bayan kiran na ta.

To amma Rasha da China da Amurka wadanda ba su cikin kasashen dake mu'amalla da kotun duniyar, sun kekashe kasa.

Karin bayani