An gano gawarwakin mutane a iyakar Enugu da Anambra

Najeriya
Image caption Rashin tsaro a Najeriya

A Najeriya, rahotanni sun ce, an gano wasu gawarwakin mutane masu yawa jibge a cikin wani rafi da ke kan iyakar jihohin Enugu da Anambra a yankin kudu maso gabashin kasar.

Yayin da wasu bayanai ke cewa, adadin gawarwakin ya kai hamsin, wani jami'in 'yan sanda ya ce ya gane wa idonsa kimanin ashirin.

Jama’a sun kwashe tsawon yinin yau suna zuwa suna kallon abin al’ajabi a rafin Ezu, wanda ya raba iyakar jihohin Enugu da Anambra

Sai dai har yanzu ba a kai ga samun cikakkun bayanai game da gawarwakin ba

Bayanai dai sun ce, an sanar da hukumomin da suka kamata, domin su sa a tsamo gawarwakin, kuma a suturta su.

Karin bayani