Algeria: Adadin wadanda suka mutu ka iya karuwa

Algeria
Image caption Garkuwa da mutane a matatar iskar gas a Algeria

Gwamnatin Aljeriya ta yi gargadin cewa akwai yuwuwar a samu karuwar adadin wadanda aka kashe cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a tashar sarrafa iskar gas din nan dake cikin hamadar Sahara.

Ministan sadarwa Muhammad Al Sa'eed ya ce akalla mutane ashirin da uku ne cikin wadanda aka yi garkuwar da su, aka tabbatar da mutuwar su, amma za a fitar da alkalumman karshe cikin sa'o'i masu zuwa.

Muhammad Sa'eed ya ce dakarun Aljeriya na musamman na cike gaba da kare masana'antar dake In-Amenas, suna kuma neman karin wasu da lamarin ya rutsa da su.

Ya kuma kara da cewa 'yan bindiga talatin da biyu wadanda aka kashe a samane da sojoji suka kai sun fito ne daga kasashe daban daban har guda shidda.

Karin bayani