Algeria: An kawo karshen masu garkuwa

Image caption Wajan da aka yi garkuwa a Algeria

Algeria ta ce dakarun ta na musamman sun kawo karshen daukin da suka kai na kwato kamfanin sarrafa iskar gas dake cikin Sahara saboda mayaka 'yan kishin Islama suna shirin yin raga-raga da shi.

Jami'ai sun ce an dana wa dukkan na'urorin kamfanin nakiyoyi.

Har yanzu dai ba a tantance yadda lamarin ya gudana ba, a karshen samamen, hukumomin Algeria sun ce mayakan 'yan kishin Islama goma sha-daya da suka rage a cikin kamfanin dukkan su sun mutu tare da mutane bakwai da suka yi garkuwa da su.

Sakataren Tsaron Amurka Leon Panetta wanda ke ziyara a London ya ce har yanzu ba su da takamaiman bayanin abinda ke faruwa.

Karin bayani