Algeria: An kama 'yan bindiga biyar

Sojojin Algeria
Image caption Ana ci gaba da bincike a cikin masana'antar iskar gas

Jami'an tsaron Aljeriya sun ce dakarun sojan kasar sun kama 'yan bindiga biyar daga cikin wadanda suka yi garkuwa da mutane a masana'antar sarrafa iskar gas dake garin In Amenas; akwai kuma uku da ake nema.

Tun da farko gwamnatin Aljeriyar ta yi gargadin cewa akwai yuwuwar adadin yawan wadanda aka kashe cikin mutanen da aka yi garkuwa da su ya karu a kan akalla ahsirin da ukun da aka bayyana.

Rahotanin kafafen yada labaran Algeria na ambaton jami'an tsaro na cewa an gano gawarwakin mutane ashirin da biyar a masana'antar gas din, amma zai yi wuya a gane ko su wanene.

Sojoji na ci gaba da bincike a masana'antar don gano ko an dana bama bamai ko kuma akwai sauran wasu da abin ya rutsa da su.

Karin bayani