Masu raayin mallakar bindiga sun yi taro

Image caption Barack Obama

Magoya bayan Kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi dake adawa da kokarin Shugaba Obama na Amurka na tsaurara matakan mallakar bindiga sun yi wani taro na kasa kan mallakar bindigar.

A hallarar da suka yi a shagunan da ake sayar da bindigogi da wurin koyon harbi sun rirrike kwafi-kwafi na kundin tsarin mulkin Amurka, suna cewa suna kare gyaran da aka yi masa ne na biyu wanda ya bayar da 'yancin mallakar bindiga.

A ranar Laraba, Shugaba Obaman ya ba da sanarwar wani shiri na sake bullo da dokar haramta mallakar bindigogin kai farmaki tare da kayyade yawan harsasai goma kacal a cikin bindiga.

Karin bayani