Mali: Afrika ta Yamma ta kammala taro

Image caption An kammala taron koli a Mali

Shugabannin kasashen Yammacin Afrika sun kammala taron kolin su game da rikicin kasar Mali tare da yin kiran karin neman goyon bayan kasashen duniya ga abinda suka kira yaki da ta'addanci.

A wata sanarwa, sun yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya ta ba su tallafin kudi da kayan aiki cikin gaggawa da za a tura dakarun yankin.

Taron kolin wanda Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius ya halarta an gudanar da shi ne a kasar Ivory Coast wadda Shugaban kasar Allasan Outtara ya kuma nemi manyan kasashen duniya su tallafa wa tsoma bakin soji da Faransa ke jagoranta a kasar Mali.

Karin bayani