Soji na sintiri a wajen garin Diabaly

Mali
Image caption Soji na sintiri a wajen garin Diabaly

Rahotanni na cewa dakarun sojan Mali da na Faransa na yin sintiri awajen garin Diabaly, kwanaki biyu bayan da masu kaifin kishin Islama suka janye daga garin da suka kwace ranar Litinin.

Magajin garin na Diabaly mai nisan kilomita dari hudu arewa da babban birnin kasar, Bamako, ya tabbatar wa da BBC cewa dakarun Mali wadanda na Faransa ke mara wa baya sun shiga garin jiya Asabar.

Ya ce sun samu konannun motoci kirar a kori kura na 'yan tawayen a kan tituna, wadanda hare haren da dakarun Faransa suka rika kaiwa ta sama suka lalata.

Dakarun Faransar na taimaka ma na Mali ne wajen kokarin dakile yunkurin 'yan tawayen na dannawa kudu, bayan da suka karbe iko da fiye da rabin kasar

Karin bayani