An rantsar da Barack Obama a wa'adin mulki na biyu

Barack Obama yana rantsuwar kama aiki
Image caption An gudanar da kwarya kwaryar biki a fadar white House

An rantsar da Barack Obama domin fara wa'adin mulkin sa na biyu a matsayin shugaban Amurka a wani kwarya kwaryan biki a fadar White House

Kundin tsarin mulkin Amurkar, ya tanaji shugaban kasa yayi rantsuwar kama aiki ne ranar 20 ga watan Janairu, amma kasancewar ranar ta fado a yau Lahadi, shugaba Obama zai maimaita rantsuwar kama aikin a gobe Litinin, a gaban dafifin jama'a a gaban ginin majalisar dokoki dake birnin Washington.

A can ne zai yi jawabi, inda zai bayyana manufofinsa cikin shekaru hudu masu zuwa.

Daga cikin kalubalen dake jiran shugaba Obama a wa'adin mulkinsa na biyu akwai sauye sauye kan dokokin mallakr bindigogi da na harkokin shigi da fici da kuma rage dimbin bashin da ake bin Amurka.