Jiragen Amurka sun kashe mutane takwas a Yemen

Jirgin Amurka marar matuki
Image caption Amurka na amfani da jirage marasa matuki wajen kai hari

Rahotanni daga Yemen na cewa wasu hare hare da aka kai da jirgin saman yakin Amurka maras matuki yayi sanadiyar kashe wasu mutane takwas, a irin hare haren da ake kai ma wadanda ake zargin mayakan kungiyar Al Qaeda ne.

Wasu makamai ne masu linzami da aka harba daga cikin jirgin saman ya fada kan wasu motoci biyu a lardin Marib, dake yankin tsakiyar kasar ta Yemen.

An ce daya daga cikin wadanda aka kashen, jagora ne na mayakan sa kai a yankin.

A cikin wata gudan da ya wuce Amurka na zafafa kai hare hare da jiragen yakin marasa matuka a Yemen, inda ake cewar kungiyar Al Qaeda na da karfi .

Karin bayani