An kai hari a ofishin Jami'an bada hannu a Afghanistan

Image caption Kai hari a Afghanistan

'Yan Kasar Afghanistan masu tayar da kayar-baya sun kai hari a hedikwatar 'yan sanda masu ba da hannu a kan tituna dake birnin Kabul.

Bayan fashewar wani dirkeken bam da aka dana cikin mota a kalla wasu mutane uku 'yan kunar bakin-wake sun kutsa kai hedikwatar wadda kusan babu mutane a cikin ta kafin wayewar gari inda suka shiga musayar wuta da jami'an tsaro.

Babban jami'in 'yan sandan kabul, Janar Ayoub Salangi ya ce an kashe biyu daga cikin maharan a yayinda a kalla daya da ya rage ake fafatawa da shi tun kimanin sa'oi biyu da fara dauki-ba-din.

Karin bayani