Mutane 37 ne aka tabbatar an kashe a Algeria- In ji Firayim minista Sellal

Abdulmalek Sellal
Image caption Mr Sellal ya ce maharan sun so ne su yi kaca-kaca da matatar iskar gas

Firayim ministan Algeria ya tabbatar da cewa, mutane talatin da bakwai da suka fito daga kasashe takwas ne aka kashe yayin kokarin kuɓutar da su bayan masu kaifin kishin Islama dake ɗauke da makamai sun yi garkuwa da su a wata matatar iskar gas.

Abdelmalek Sellal ya ƙara da cewa, har yanzu ana kokarin gano wasu 'yan ƙasashen waje biyar da suka ɓata.

Ya kuma ce masu fafutukar dake dauke da muggan makamai sun so ne su yi amfani da bama-bamai wajen yin kaca-kaca da matatar iskar gas ɗin da suka mamaye a Gabashin ƙasar.

Wakilin BBC ya ce Mr Sellal ya ce an hallaka yawancin 'yan ƙasashen wajen da aka yi garkuwa da su ne ta hanyar harbi da bindiga a ka.

Karin bayani