Majalisar dokokin ƙungiyar ECOWAS ta goyi bayan tura sojoji Mali

Kadre Desire Ouedrago
Image caption Kadre Desire Ouedrago

Majalisar dokokin ƙungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta tabbatar da goyon bayanta ga matakin da ƙungiyar ta dauka na tura sojoji Mali don ƙwato yankin da 'yan tawaye suka mamaye.

Majalisar dokokin ta ce ya kamata dakarun ƙungiyar da sauran masu tallafa musu su tsaya wajen ganin cewa 'yan tawayen ba su auka wa wasu ƙasashen da ke makwaɓtaka da Mali ba.

Majalisar dokokin ECOWAS din ta yi zama na musamman ne a Abuja, inda mambobin majalisar suka yi nazarin abin da ke faruwa a Ƙasar ta Mali da kuma matakin da ƙungiyar ta dauka na tura sojoji fiye da dubu uku don fatattakar 'yan tawayen da suka kame Arewacin ƙasar.

Majalisar ta kuma buƙaci hukumar Ecowas da shugabannin ƙasashe 'ya'yan ƙungiyar, da ƙungiyar tarayyar Afirka da kuma majalisar ɗinkin duniya da su ɗauki dukkan matakan da za su taimaka wajen daƙile yunƙurin 'yan tawayen a Mali.

Karin bayani