Sojojin Faransa sun shiga garin Diabaly

Dakarun Faransa
Image caption Kimanin dakarun Faransa 2,000 ne a kasar ta Mali

Jami'ai sun ce dakarun Faransa da na Mali sun shiga garin Diabaly na tsakiyar kasar ta Mali mai muhimmanci ba tare da wata turjiya daga mayakan 'yan tawaye ba.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce kimanin motocin soji 30 ne dauke da dakarun Faransa da na Mali 200 suka shiga garin.

Masu kishin Islama sun fice daga garin ranar Juma'a bayan da dakarun Faransa suka yi masa lugudan wuta.

Faransa ta kaddamar da hare-haren soji kan Mali fiye da mako guda da ya gabata domin kawo karshen mamayar da 'yan tawaye suka yi wa arewacin kasar.

Dakarun Faransa 2,000 ne suka isa Mali domin yakar 'yan tawayen, wadanda ake alakanta wa da kungiyar Al ka'ida a yankin Magrib.

Sannan suka bukaci dakarun kasashen yammacin Afrika da su gaggauta shirin da suke na tura sojojin yankin fiye da 3,000.

Izuwa ranar Lahadi dai kimanin dakarun Afrika 150 ne suka isa Bamako babban birnin na Mali, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

Karin bayani