An tuhumi Charles Ble Goude a Ivory Coast

Charles Ble Goude
Image caption Charles Ble Goude ya musanta dukkan zargin da ake ma shi

An tuhumi wani tsohon jagoran matasan Ivory Coast da aikata laifukan yaƙi saboda irin rawar da ya taka yayin tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban ƙasar shekaru biyu da suka gabata.

An kuma tuhumi Charles Ble Goude da aikata kisa da kuma satar dukiyar gwamnati.

Sai dai kuma ya musanta dukkan zargin.

An dai kama Mr Ble Goude ne a Ghana cikin makon jiya, kana aka tisa keyarsa zuwa ƙasar ta Ivory Coast.

Ya rike muƙamin ministan kula da matasa a cikin gwamnatin Laurent Gbagbo, wanda ya ƙi ya sauka daga kan karagar mulki bayan zaɓen shekara ta 2010, abun da ya haddasa yaƙin basasa a ƙasar inda mutane fiye da dubu uku suka rasa rayikansu.