An gurfanar da masu fyade a India

India
Image caption Fyaden ya haifar da zanga-zanga mai muni a kasar ta India

Mahaifin yarinyar nan 'yar India da aka yiwa fyade har ta kai ga mutuwa a birnin Delhi cikin watan jiya ya ce, marigayiyar ta so ne a rataye wadanda suka yi ajalinta.

Ya shaida wa BBC hakan ne yayin da aka gurfanar da wasu mutane biyar da ake zargi da aikata fyaden a gaban wata kotu mai aiki cikin gaggawa.

Hukumomi a India, sun ce, sun samu isassun shaidu da da za su kai su ga hukunta wadanda ake zargi, kuma suna son su gaggauta kammala shari'ar cikin sauri.

Ana dai shari'ar ne a wata kotu ta musamman da aka kafa domin shari'un da suka danganci fyade a kasar.

Wanna batu ya yi matukar girgiza India, ya kuma janyo mahawara akan yadda ake mu'amala da mata.

An samu tsaiko a fara gabatar da shari'ar ne saboda tattaunawar da masu shari'a da lauyoyi suka yi.

Daya daga cikin lauyoyin na bukatar a dauke sauraren shari'ar daga birnin Delhi.

VK Anand shi ne lauyan da ke kare Ram Singn, ya ce irin yadda kafafen yada labarai ke zuzuta abin ka iya janyowa ayi rashin adalci a shari'ar, ya kuma kara da cewa sun tabbatar ba za ayi musu adalci a Delhi ba.

Sauran wadanda ake zargi sun hada da kanin lauya Mr Singh mai suna Mukesh, da Pawan Gupta, da Vinay Sharma, da kuma Akshay Thakur, na cikon shidan yaro ne dan shekara sha bakwai.

A bangare daya kuma mahaifiyar yarinyar da aka yiwa fyaden ta yi Allah wadai da tsokacin da wasu ke yi na cewa 'yar ta ita ce ta janyo aka yi mata wannan aika-aika.

Ta shaidawa BBC cewa wadanda suka bayyana wannan ra'ayi ba su san ya kamata ba, kuma sun goyi bayan irin wannan aika-aika.

Wasu masu zanga-zanga sun taru a wajen kotun a yau, inda suka bayyana cewa an yi rashin adalci akan wannan tsokaci.