An rusa wata gada mai muhimmanci a Mali

Sojojin Mali
Image caption Sojojin Mali da na Faransa na ci gaba da farautar 'yan tawaye

'Yan tawayen Ansaruddin a kasar Mali sun rusa wata gada mai muhimmancin gaske da ta hada gabashin kasar da jamhuiryar Niger.

Katse gadar dai ya yanke hanyar kaiwa ga garin Gao inda 'yan tawayen suke da karfi sosai kuma daya daga garuruwa mafi muhimmanci da ke Arewacin kasar.

Rahotanni dai sun ce mayakan Islama sun yi raga-raga da gadar ce ta Tassiga ta hanyar amfani da nakiyoyi.

Wani dan kasuwa da ke harkar sufurin motoci, ya shaida wa kamfanin dilacin labaran Faransa cewa yanzu babu wanda zai iya zuwa Nijar ko kuma garin Gao daga garin Tassiga.

Ci gaba da sintiri

Wata majiyar tsaro daga Jumhuriyar ta Nijar ma ta tabbatar da labarin lalata gadar ta Tassiga, tana mai cewa tun safiyar ranar Juma'a, babu wata mota da ta tashi daga yankin kan iyakar Nijar din zuwa garin Gao.

Garin na Tassiga yana da nisan kilomita 60 ne daga iyakar Nijar.

Wannan al'amari dai ya faru ne yayin da sojojin Chadi 2000 da na Nijar 500 ke shirin tsallakawa cikin Mali daga kasar ta Nijar, domin bude wani fagen daga a Gabashin kasar a ci gaba da fafatawar da sojojin Faransa da na Mali ke yi da masu fafutikar Islama.

Jiragen yakin Faransa sun kai farmaki ranar Alhamis da daddare a kan sansanin masu fafutika a garin Ansongo mai nisan kilomita 40 daga garin Tassiga, kuma sojojin Faransa da na Mali na ci gaba da sintiri a yankin.