Mali: Sojin Faransa na kokarin mayarda iko ga gwamnati

Image caption Dakarun sojin Faransa a Niono

Ministan tsaron Faransa Jean Yve Le Drian ya ce tsoma bakin sojojin kasar sa a kasar Mali na da nufin mayar da ikon daukacin kasar ga gwamnati ne.

Yace harin da Faransar a yanzu take kaiwa tana lugudan wuta ne kan wasu yankuna na Gao da Timbuktu a sashen da mayakan 'yan kishin Islama suka mamaye.

Mr Le Drian ya amsa cewar har yanzu sojojin na Faransa ba su kwato ikon mulkin Diabaly baki daya ba, amma yace nan da wasu 'yan sa'oi za a kwace shi.

An ba da rahoton cewar 'yan kishin Islamar sun janye daga garin a ranar Jumma'a bayan ruwan bama-bamai daga sojojin Faransa.

Karin bayani