'Yan tawayen Mali sun rabu gida biyu

"Yan tawayen Mali sun rabu gida biyu"
Image caption Sojojin Faransa na ci gaba da yakar 'yan tawayen

Rahotanni daga Mali sun ce 'yan ƙungiyar Ansarud Din da suka kama yanki mai yawa a arewacin kasar, sun rabu gida biyu.

Kuma bangaren da ya ballen yana son tattaunawar zaman lafiya.

A cikin wata sanarwa, sabuwar ƙungiyar, wadda ta kira kanta Ƙungiyar Islama ta Azawad, ta ce ba ta goyi bayan zafin ra'ayi ba, tana kuma son warware al'amurra ta hanyar tattaunawa.

Faransa ta tura sojoji zuwa Mali a farkon wannan watan domin dakatar da mamayar da 'yan tawaye ke yi wa yankunan kasar.

Ta ce 'yan tawayen na da alaka da ƙungiyar Alƙa'ida - kuma wasunsu 'yan ƙasashen waje ne.

Sannan ta ƙara da cewa 'yan tawayen na barazanar mayar da Mali kasar 'yan ta'adda.

A watanni goma da suka gabata, ƙungiyoyin Islama uku ne ke iko ga arewacin Mali inda suka kafa tsarin shari'ar Islama.

Karin bayani