Obama ya nemi Amurkawa su tashi tsaye

Barack Obama
Image caption Akwai dai gagarumin kalubale ga shugaba Barack Obama

Barack Obama ya shaida wa Amurkawa cewa su yi "amfani da damarsu", a wani jawabi da ya yi a birnin Washington DC lokacin da yake shan rantsuwa domin fara zagaye na biyu na shugabancin kasar.

Yace damar da Amurka keda ita ba ta da iyaka bayan shekarun da kasar ta shafe tana yaki da kuma matsalar tattalin arziki.

Sai dai ya ce shekaru goma na yaki suna zowa karshe, kuma tattalin arzikin kasar ya soma farfadowa.

Mr Obama, mai shekaru 51, wanda shi ne shugaban Amurka na 44, ya sha rantsuwa ne ta hannun alkalin alkalan kasar John Roberts.

Dubban daruruwan mutane ne suka cika dandalin taro na National Mall domin halartar bikin.

Tsohon shugaban kasa Bill Clinton da Jimmy Carter, tare da wasu sanatoci da 'yan majalisar wakilai da dama da sauran manyan baki sun halarci bikin.

Muhimman batutuwa na kasa

Tun da farko an rantsar da shi a wani kwarya-kwaryar biki a fadar White House ranar Lahadi - tsarin mulkin kasar ya ce wajibi ne shugaba ya fara aiki ranar 20 ga watan Janairu.

Shugaba Obama ya shaida wa mahalatta taron cewa ya dau ranstuwa ne da sunan Ubangiji da kuma kasar - ba wai da sunan jam'iyya ba.

Ya ce kamata ya yi Amerika ta kara tsayawa a kan manufofin da aka santa da su - na kare rai, da 'yanci da kuma rayuwa ta gari.

"Bari mu tashi tsaye domin tabbatar da tarihi," a cewar Obama lokacin da yake kammala jawabin na sa.

A fitaccen dakin taron nan na Blue Room tare da matarsa da kuma 'ya'yansa mata biyu, shugaban ya dora hannunsa akan littafin Bible na mabiya addinin Kirista wanda iyalan Michelle Obama suka shafe shekaru suna amfani da shi, a lokacin da yake karbar rantsuwa daga mai shari'a Roberts.

Bikin rantsuwar dai ya hada da kada-kade da wakoki, inda mawakiyar nan Beyonce ta rera taken kasar Amurka a karshe.

Karin bayani