Obama zai sha rantsuwar kama aiki

Shugaba Obama zai gatabar da jawabin rantsar da shi yayin da yake shirin soma wa'adin mulki na biyu.

Jiya ne dai shugaba Obama yayi rantsuwar kama aiki a fadar White House, kuma zai sake yin rantsuwar a bukin da jama'a cigaba da hallara yanzu haka.

Dubban mutane ne dai ake sa ran zasu halarci bukukuwan.

To ko mutanen Amurka bakaken fata da galibi Shugaba Obaman ne suka zaba sun gamsu da rawar da ya taka zuwa yanzu.