Kotu ta samu Okah da laifin aikata ta'addanci

Image caption An samu Henry Okah da laifin dasa bam a Abuja a shekarar 2010

Wata kotu a kasar Afrika ta kudu ta samu dan Nigeriya Henry Okah da aikata laifuka goma sha uku da su ka danganci ta'adanci.

Laifukan dai sun hada da dasa bam-bamai a birnin Abuja a ranar murnar samu cin gashi kai a shekarar 2010, wanda kuma ya yi sanadiyar hallaka mutane 12.

"Saboda irin shaidun da aka gabatar a gabana, bani da shakka cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin da ake zarginsa da aikatawa." In ji Alkali Neels Claassen a lokacin da ya ke yanke hukunci a babbar kotun da ke kudancin Gauteng.

An dai samu Okah da kitsa shirya hare-hare ta hanyar amfani da motoci biyu da aka shiryawa bama-bamai inda mutane goma sha biyu su ka rasa rayukansu a birnin Abuja a ranar daya ga watan Okutoban shekarar 2010 da kuma tayar da bama-bamai a watan Maris din shekarar ta 2010 a garin warri dake jihar Deltan a kudu maso kudancin Najeriya.

Kungiyar dake fafutukar kwato yancin yankin Niger Delta wato MEND ce tayi ikirarin kaddamar da harin a wannan lokaci.

Okah dai ya musanta cewa yana da hannu a hare-haren da aka kaddamar inda ya ce ana tuhumarsa ne da wata manufa ta siyasa.

Har wa yau, ya musanta cewa shi ke shugabancin kungiyar MEND, amma dai ya nuna cewa yana goyon bayan ayyukan kungiyar.