Charles Taylor zai daukaka kara

Image caption Charles Taylor zai daukaka kara

Tsohon Shugaban Liberia Charles Taylor zai fara daukaka kara a yau Talata, a kan tuhumar da aka yi masa ta aikata laifukan yaki da hukuncin da Kotun musamman da Majalisar Dinkin Duniya ke rufa ma baya ta yanke masa na shekaru hamsin da daya.

An samu Mr Taylor din ne da laifi a bara na ba wa 'yan tawaye makamai a makwabciyar kasar Saliyo wadanda suka rinka ba shi lu'u-lu'u da ake hakowa a yankunan dake hannun 'yan tawayen.

Lauyoyin da suka shigar da kara za su nemi Kotun dake birnin Hague ta kara tsawaita hukuncin da aka yanke wa Mr Taylor don ya dace da abin da suka kira mu'nin laifukan da ya aikata.

Karin bayani