Rashin aikinyi ya karu a duniya - ILO

Image caption Kungiyar Kwadago ta Duniya ILO

Kungiyar Kwadago ta Duniya ILO ta ce adadin maras sa aikin yi a fadin duniya ya karu da fiye da mutane miliyan hudu a bara, abin da ya nuna durkushewar tattalin arziki.

Lamarin ya fi muni ne tsakanin matasa a kasashen da suka cigaba..

Kungiyar kwadagon ta ce akwai matasa masu neman aiki 'yan kasa da shekaru ashirin da hudu da suka gaza samun aikin.

Ta yi kira da a kara saka jari a bangaren horar da sana'oin hannu don baiwa matasa damar samun abin yi.

Tace kasashen da ba su yi sako-sako ba da cibiyoyinsu na koyar da sana'oin hannu, irinsu Jamus da Austria da Switzerland su ne ke da karancin matasan da ba su da abin yi.

Karin bayani